Rahoton wanda wata cibiyar tsaro ta Beacon Consulting, ta fitar ya nuna cewa al’amuran rashin tsaro da kashe-kashe sun yi ƙamari a cikin wannan shekara, inda aka kashe mutane dubu 7,544 tare da garkuwa da mutum dubu 6,453 tsakanin watan Janairu zuwa Satumba.
Rahoton cibiyar ya nuna yadda aka samu ƙaruwar tashe tashen hankulan da ya shafi kananan hukumomi 667 na ƙasar, wanda ta alakanta su da ta'addanci da ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya, da dai sauran nau'ikan tada zaune tsaye.
Masana dai na nuna damuwarsu kan kalubalen tsaro da ke kara ta'azzara, sun kuma yi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki kwararan matakai.
Haka na gaji matsalar tsaro - Tinubu
A wani taron tsaro da zaman lafiya da ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma suka shirya a jihar Katsina a watan Yuli, Shugaba Tinubu ya bayyana rashin tsaro da ake fama da shi musamman a yankin Arewa maso Yamma a matsayin wanda ya gada daga gwamnatotin baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI