Wannan ta faru ne bayan da ƴan bindigar suka hana gawarsa tare da ikirarin yi masa sutura a cikin daji.
Majiya daga iyalan sarkin tace duk da ƴan bindigar sun kashe Sarkin sai da suka karɓi Naira miliyan 60 da babura guda 5 ɗin da suka buƙata a matsayin kuɗin fansa kafin su saki ɗansa mai suna Kabiru da suka kama su tare da mahaifin sa.
Kawo yanzu dai ana raɗe-raɗin cewa ɗan nasa Kabiru ya gamu da ruɗewar kwakwalwa sakamakon tashin hankalin da ya gamu da shi a cikin dajin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI