Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Jaridar Daily Trust da ake wallafa a ƙasar cewa, ƴan bindigar sun kai hari ƙauyen ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Lahadi.
Mun ƙirga mutane 43 ciki har da maza magidanta 3 da mata da yara 40 ne ƴan bindigar suka sace.
Majiyar ta ce a jiya Litinin ne suka gudanar da ƙididdigar waɗanda aka yi garkuwa da su, kuma har yanzu maharan basu ƙira kowa don sanarsu halin da ake ciki ba.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta’addan sun kai hari ƙauyen ne ɗauke da muggan makamai, lamarin da ya tilastawa magidanta maza tserewa cikin daji don neman mafaka.
Haka nan wata majiya daga ƙauyen ta ce ƴan bindigar sun bi gida-gida ne suka tattara mutanen da suka yi garkuwa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI