An gano gawarwaki 191 na fasinjojin jirgin ruwan 'yan maulidi a Neja

An gano gawarwaki 191 na fasinjojin jirgin ruwan 'yan maulidi a Neja

 

'Dan Majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazabar Kaiama, karamar hukumar da fasinjojin suka fito Saidu Baba Ahmed ne ya tabbatar wa da RFI Hausa hakan a safiyar yau, inda ya kara da cewa mutune 92 ne kawai aka iya cetowa a raye daga cikin fasinjoji 285 da suka shiga jirgin ruwan. 

Wasu masu aikin ceto bayan kifewar jirgin ruwan da ya taso daga Neja zuwa jihar Kebbi a arewacin Najeriya. Wasu masu aikin ceto bayan kifewar jirgin ruwan da ya taso daga Neja zuwa jihar Kebbi a arewacin Najeriya. © Daily Trust

Sai'idu wanda ya ce tare da shi aka yi jana'izar gawarwakin da aka gano, ya kara da cewa a halin yanzu mutane biyu ne ba a gan su ba daga cikin fasinjojin jirgin. 

Hatsarin dai ya faru ne a ranar Litinin 1 ga watan Oktoba da misalin karfe 8 na dare bayan fasinjojin wadanda galibinsu mata ne da kananan yara sun bar garin Gbajibo na jihar Kwara zuwa Gbajibon a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.

Tasiwrar Najeriya da ke nuna jihar Neja. Tasiwrar Najeriya da ke nuna jihar Neja. © Wikimedia Commons

Gwamnatin jihar Kwara wadda ta tura tawaga ta musamman karkashin jagorancin Kakakin Majalisar dokokin jihar, Yakubu Danladi Salihu a jiya Asabar ta ziyarci garin domin jajanta wa al'ummar kauyen Gbajibon jihar da masarautar Kaima bisa faruwan wannan Iftila'i. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)