Wasu daga cikin jihohin da yajin aikin ya shafa sun haɗa da Cross River, Enugu, Nasarawa, Katsina, da Sokoto da Zamfara sai kuma Kaduna.
A zantawar Rfi Hausa da Shugaban ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar NLC reshen jihar Kaduna, Kwamred Ayuba Magaji Suleiman, domin jin halin da ake ciki ya bayyana cewa ma'aikatan sun yi biyayya ga Uwar ƙungiyarsu ta ƙasa wajen tsunduma yajin aikin.
Kwamred Ayuba ya ce sun yi hakan ne domin bai wa ma'aikatansu kariya kamar yadda doka ta tanada, kuma da yawa daga cikin ma'aikata ba su fito aiki ba.
Sai dai ya ce har yanzu babu wani martani daga bangaren gwamnati game da yajin aikin da suka tsunduma, amma ƙofarsu a buɗe ta ke domin tattaunawar samun masalaha.
Tun a ranar 10 ga watan Nuwamban da ya gabata ne dai NLC ta bayar da wa'adin ranar 1 ga watan Disambar da muke ciki, kafin shiga yajin aikin gargaɗi a jihohin Najeriya da suka ƙi amincewa da biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Tuni dai wasu ma'aikata a jihohin ƙasar suka fara karɓar mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya sanya su darawa, yayin da wasu gwamnatocin jihohin suka amince da biya amma basu fara aiwatarwa ba.
An kai ruwa rana dai kafin a sasanta tsakanin gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da shugabannin Ƙungiyoyin Kwadago na NLC da TUC game da tsaida mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI