Ƴan fafutuka na neman haƙƙin yaran da aka ɗaure tsawon kwanaki 93 a Najeriya

Ƴan fafutuka na neman haƙƙin yaran da aka ɗaure tsawon kwanaki 93 a Najeriya

Rahotanni sun ce ministan shari’ar Najeriyar Prince Lateef Fagbemi ya bukaci mika masa takardun shari’ar yaran zuwa ofishinsa don bin kadinsu.

Tuni dai wannan batu ya haifar da cece kuce a fadin kasar, musamman lura da yadda yaran suka shafe kwanaki 93 a hannun jami'an tsaron a gefe guda Kotu ta nemi kowannensu cikin yaran su fiye da 70 masu ƙarancin shekaru su biya belin miliyan goma goma.

Hotunan yaran su 125 yayin bayyanarsu a gaban kotun sun nuna yadda matsananciyar yunwa ta galabaitar da su tare da fitar da su daga hayyacinsu, batun da ya haddasa cece kuce tsakanin al'ummomin sassan arewacin ƙasar.

Mahukuntan Najeriyar dai sun ce suna tuhumar ƙananun yaran da laifukan masu alaƙa da cin amanar ƙasar bayan zanga-zangar yunwar da suka shiga don ƙalubalantar salon kamun ludayin gwamnatin ƙasar da ya tsawwalawa jama'a tare da haddasa tsadar rayuwa.

Sai dai ƴan fafutuka irin daraktan Amnesty International a Najeriya Malam Isa Sunusi na ganin hatta bayan sakin yaran dole ne mahukuntan Najeriya su biya su hakkin lalata musu rayuwa da aka yi sakamakon tsarewar da aka musu wadda ta saɓawa doka.

Ƙarƙashin dokokin Najeriya dai sa'o'i 48 ne kaɗai aka sahalewa hukumar ƴansanda ta iya tsare mai laifi a hannunta gabanin miƙa shi ga kotu, sai dai a kusan kowanne mataki na ƙasar ana yiwa dokar karan tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)