Bayanan masu tayar da hankali na zuwa a dai dai lokacin da wasu majiyoyi ke cewa ɗan bindigar daji Dogo Giɗe ya sanyawa wasu garuruwa 23 a ƙaramar hukumar tsafe duk cikin jihar ta Zamfara harajin naira miliyan 100 bisa sharaɗin kai musu hari matuƙar suka gaza haɗa adadin kuɗin da ya nema, ko da ya ke a zantawar da sashen Hausa na RFI ya yi da mazauna yankin sun ce babu batu mai kama da wannan barazana.
Kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya sun ruwaito yadda gomman ƴan bindigar suka farmaki garin Gana a jihar Zamfara cikin ranakun ƙarshen mako tare da buɗe wuta kan jama'a wanda ya kai ga ƙone tarin gidajen da wuraren sana'ar jama'a gabanin sace tarin mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Wannan hari na zuwa bayan makamancinsa a watan da ya gabata, wanda shi ma ya kai ga sace tarin mutane, a wani yanayi da ake ganin dawowar makamantan hare-haren da kuwa garkuwa da mutane.
A lokuta da dama jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da nanata cewa sun kame tarin jiga-jigan masu garkuwa da mutane a wannan jiha, yayinda suke neman wasu ruwa a jallo.
Kusan dukkanin jihohin yankin na arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar matsalolin ɓatagarin kama daga ƴan bindiga da kuma ƴan ta'addan waɗanda suka hana jama'a sakat tare da kassara harkokin noma da kasuwanci, lamarin da ya ta'azzara talauci da yunwar da al'umma ke fama da ita.
Ko a makon da ya gabata, sai da ƴan bindigar, suka tare wata motocin safa tare da banka mata wuta bayan sace ilahirin fasinjan da ke cikinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI