Majiyoyi daga yankin da lamarin ya faru sun bayyana cewa, ƴan bindigar sun yi nufin ƙaddamar da farmaki ne kan wata makarantar firamari da ke garin na Kuyello, amma suka tarar cewa, ɗalibai ba su koma sabon zangon karatu ba.
Rashin tarar da ɗaliban ne ya sanya ƴan bindigar karkata harinsu kan malaman jinya da ke aiki a wani asibiti daura da makarantar firamarin.
Ɗaya daga cikin shugabannin yankin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin mai tayar da hankali.
Sun isa yankin, suka nufi makarantar, suna zaton cewa za su tarar da ɗalibai. Sai dai babu kowa a makarantar. Hakan ya sa suka wuce kai tsaye zuwa asibitin Kuyello, suka sace malaman jinya mata.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko ƴan bindigar sun sace hatta marasa lafiyar da ke jinya a asibitin.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin, babu wani martani da muka samu daga ɓangaren gwamnatin jihar Kaduna ko kuma jami'an ƴan sanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI