Ƴan bindiga sun mamaye sansanin horon soji mafi girma a Najeriya - Majalisar Neja

Ƴan bindiga sun mamaye sansanin horon soji mafi girma a Najeriya - Majalisar Neja

Ƴan majalisar sun ce ayyukan ƴan bindigar sun raba al'ummomi 23 da ke kewayen sansanin sojin Nagwamase a hedikwatar karamar hukumar Kontagora.

A cewar ƴan majalisar, sansanin shine na horas da sojoji mafi girma a Najeriya.

Majalisar ta ce ƴan bindiga sun karbe sansanin inda ta bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta hada kai da hukumomin soja domin fatattakar su.

An gabatar da wannan batu ne a gaban ƴan majalisar ta hanyar wani kuduri mai muhimmanci da dan majalisar mai wakiltar mazabar Kontagora 11, Abdullahi Isah, ya gabatar a zaman majalisar a ranar Talata.

Mista Isah ya ce yanzu haka ƴan bindigar da suka shigo daga wasu yankunan sun mamaye sansanin sojoji, wanda ya taso daga karamar hukumar Kontagora har zuwa karamar hukumar Mariga.

Dan majalisar ya sanar da abokan aikinsa cewa tun lokacin da ƴan bindigar suka karbe sansanin horon, al'ummominn manoma 23 sun kauracewa matsugunansu saboda yawaitan hare-haren da ƴan bindigar ke kaiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)