Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ne ya sanar da hakan, bayan da ya samo kofin wasikar da hukumomin tara bayanan sirri daga Zamfara suka tura wa takwarorinsu da ke Kano.
A cewar AFP, tun a ranar litinin da ta gabata ne aka gabatar wa gwamnan jihar Kano da wannan rahoto, da ke cewa mafi yawan ‘yan bindigar tuni suka mallaki gidaje a cikin birnin Kano, yayin da wasu ke fakewa a unguwannin Rijiyar Zaki, Tudun Yola, Jaen, Dorayi Babba, Rijiyar Lemo da kuma Yan Awaki.
Bisa ga dukan alamu, rahoton ya ce mafi yawan ‘yan bindigar sun nemi mafaka a birnin Kano ne saboda tsanantar hare-hare da jami’an tsaro ke kai musu a cikin ‘yan kwanakin nan, yayin da wasu suka mallaki gidajen tsawon shekaru a birnin a daidai lokacin da suke taimaka wa ‘yan bindigar da ke gudanar da ayyukan tsagarenci a jihohin Zamfara, Katsina da kuma Kaduna.
Wasu majiyoyi biyu na tsaro, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran AFP da cewa rahoton ya shiga hannuwansu, yayin da wata majiyar ke cewa yanzu tana aiki tukuru domin zaƙulo su a cikin gaggawa.
To sai dai majiyar ke cewa yanzu haka jami’an tsaro na aiki ne a asirce domin ka da su jama’a su shiga hali na firgita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI