Wasu mazauna yankunan da aka kai harin da suka yi magana da jaridar Dailytrust sunce an kashe sama da mutum 30.
Waɗanda ƴan bindigar suka kashe sun dawo ne daga gaisuwar mutuwa a Batsari a lokacin da ƴan bindiga suka auka musu.
Harin ƴan bindigar ya faru a ƙauyen Ɓaure da ya ke zama wani babban wuri da ƴan bindiga ke aikata ta’addanci.
Jama’ar da ke rayuwa a ƙauyukan Barebari a karamar hukumar Safana da basu amince a ambaci sunansu ba sunce mutum 15 ne suka mutu a wurin da aka kai harin.
Mazauna yankin sun ce ƴan bindigar sun ƙona mutane ƙurmus kuma akwai waɗanda ba’a san inda suke ba.
Wani mazaunin yankin na daban ya ce sun samu nasarar ceto mutum 20 da suka fito daga garuruwan Charanci da Burji da Jibiya da kuma Kaita, ya kuma tabbatar da cewa mutum 25.
Daga cikin waɗanda aka kashe a harin har da masu aikin sa kai na bijilanti.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI