Rahotanni sun ce mutanen su 7 sun je ɗakko amfanin gobarsu ne lokacin da ƴan bindigar suka far musu inda suka hallaka su baki ɗaya tare da ƙone masarar da suka loda a babbar motar ɗaukar kaya da bayanai ke cewa yawanta ya kai bugu 50.
Wani ganau ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, ƴan bindigar sun laɓe ne har sai da suka jira mutanen sun kammala loda masarar a cikin mota kafin nan suka buɗe musu wuta tare da ƙone motar baki ɗaya.
A damunar bana ƴan bindigar da suka addabi jihohin arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya sun fitar da wani salon ƙone amfanin gona wanda ke ci gaba da ta’azzara a baya-bayan nan.
Daga lokacin da aka fara girbe kawo yanzu anga faruwar makamancin ta’addancin na ƙone amfanin gona da ƴan bindigar ke yi jihohi irin Zamfara da Kaduna da kuma Sokoto baya ga jihar ta Neja.
Wannan salon ta’addanci na ƴan bindigar na zuwa ne a dai dai lokacin da matsalar yunwa ke ci gaba da ta’azzara a sassan Najeriya sakamakon rashin samun wadataccen amfanin gona wanda ke da nasaba da yadda ambaliya ta yiwa tarin manoma ɓarna.
Jihohin Neja da Zamfara waɗanda a baya ke iya samar da wadataccen abinci ga al’ummominsu tun bayan tsanantar ayyukan ƴan bindiga ƙauyuka da dama sun zama kufai yayinda manoma suka haƙura da gonakinsu don tsira da rayukansu, ko da ya ke rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da iƙirarin fatattakar ƴan bindiga a jihohin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI