Cikin wani rahoto da ta fitar a makon nan wanda ta sanya sunan ‘Tattalin arziƙin ma’aikatar garkuwa da mutane a Najeriya’ SB Morgan ta ce ƴan bindigar da ke garkuwa da mutane don neman fansa a Najeriya sun nemi a biya su tsabar kuɗi har naira biliyan 10 da miliyan 900 don fansar ƴan uwa da iyalan mutanen da suka kame a tsakanin wa’adin na watan Yunin 2023 zuwa Yulin 2024.
Sai dai a cewar ƙungiyar iyalai da ƴan uwan mutane basu iya bayar da dukkanin kuɗin da ƴan bindigar suka nema ba, ko da ya ke sun biya kuɗin da yawansu ya kai naira biliyan 1 da miliyan 48 a ɗan tsakanin.
Ƙungiyar ta SBM wadda ke tattara bayanan halin da yanayin tsaro ya ke a nahiyar Afrika, cikin bayanan da ta wallafa a shafinta game da yanayin tsaron Najeriya, ta ce ƙasar ta yammacin Afrika mafi ƙarfin tattalin arziƙi da yawan jama’a a nahiyar na matsayin kan gaba a abin da ya shafi rashin tsaro ta fuskar garkuwa da mutane.
A cewar SBM aƙalla mutane dubu 7 da 568 aka sace a hare-hare dubu 1 da 130 da ƴan bindiga kan kai kan jama’a tsakanin watan na Yunin bara zuwa Yulin bana.
Rahoton na SBM ya bayyana yadda tsaron Najeriya ke ci gaba da taɓarɓarewa yawaitar ɓatagari masu riƙe da makamai kuma ke ta’azzara.
SBM ta ce matsalar garkuwa da mutane don neman fansa ta zama gama gari a sassan Najeriya wanda tarin matsalolin tsaro suka haifar kama daga boko haram a yankin arewa maso gabashin ƙasar da ƴan bindiga a tsakiyar arewa da arewa maso yamma baya ga ayyukan tsageru da ƴan ta’adda a kudu maso gabas da kuma dabanci da babakere da ya dabaibaye kudu maso yammacin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI