Rahotanni sun ce a ranar Asabar ɗin da ta gabata ne ƴan bindigar sun farmaki gidan Surajo Amadu ne da ke ƙauyen Mai Rana a ƙaramar hukumar Kusada ta jihar Katsinar inda suka hallaka shi nan ta ke suka kuma sace matarshi guda da ƴar shi.
Ƙungiyar ta Miyetti Allah a ƙasa baki ɗaya ta tabbatar da kisan Surajo wanda ta ce kisan ya zo a sai dai lokacin da aka cika watanni 22 da kisan wancan shugaban da ya gabace shi wato wanda shima ƴan bindigar suka sace shi kuma har zuwa yanzu ba a kai ga gano gawarshi ba.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Katsina ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa jami’ansu sun kai ɗaukin gaggawa wajen da harin ya faru amma tun gabanin isa da Surajo asibiti rai ya yi halinsa, sai dai ya ce yanzu haka suna ƙoƙarin don ganin sun kuɓutar da iyalinshi da ke hannun ɓatagarin.
Bayanai sun ce baya ga shugaban na Miyetti Allah akwai kuma wasu mutum biyu da ƴan bindigar suka hallaka nan ta ke yayin harin na ranar Asabar.
Watanni 3 kenan cif da naɗin sabon shugaban na Miyetti Allah a jihar Katsina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI