Amurka ta musanta zargin ɗaukar nauyin ta'addancin Boko Haram a Najeriya

Amurka ta musanta zargin ɗaukar nauyin ta'addancin Boko Haram a Najeriya

Jakadan Amurkan a Najeriya, Richard M. Mills Jr. da ke kawar da wannan zargi gaban manema labarai jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da ya yi tare da gwamnonin jihohin Najeriya 36 ya ce Amurka ba ta hannu a ƙungiyar Boko Haram, hasalima ta na taimakawa Najeriya don ganin ta kawar da matsalar.

Jakadan Amurka a Najeriya, Richard M. Mills Jr. Jakadan Amurka a Najeriya, Richard M. Mills Jr. © RFIHAUSA

Tun farko ɗan Majalisar Amurka na jam’iyyar Republican da ke wakiltar Pennsylvania Scott Perry ne ya yi iƙirarin cewa hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID ce ke ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashe ciki har da Boko Haram ta Najeriya.

A ƙoƙarinsa na kare manufar shugaba Donald Trump game da rushe hukumar USAID, Scott ya ce kaso mai yawa na kuɗin da ake tattarawa da sunan tallafi suna ƙarewa ne a hannun ƴan ta’adda irin ISIS da Al-Qaeda sai kuma boko haram kana ISIS Khorasan.

A cewar Mills Jr, babu wata hujja da ke nuna Amurka na goyon bayan ta’addanci a Najeriya, hasalima akwai tarin hujjoji da ke tabbatar da yadda ta ke taimakawa ƙasar wajen magance matsalolin tsaron da suka fabaibayeta.

Jakadan na Amurka a Najeriya ya ce idan Washington ta samu ko da ƙaramar hujja ce da ke nuna ana karkatar da kuɗaɗen tallafin USAID ko sauran ƙungiyoyi da hukumomin Amurka zuwa ayyukan ta’addanci, ko shakka babu za su jagoranci bincike da haɗin gwiwar Najeriya don hukunta masu hannu a badaƙalar.

Ƙungiyar ta’addancin ta Boko haram ta shafe tsawon shekaru aƙalla 15 a yankin arewa maso gabashin Najeriya da wasu sassa na Chadi da Nijar da Arewacin Kamaru da kuma Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)