Amurka ta bayyana takaici kan yawaitar tauye hakkin yin addini a Najeriya

Amurka ta bayyana takaici kan yawaitar tauye hakkin yin addini a Najeriya

Hukumar ta USCIRF ta bayyana cewa bayanan da ta tattara sun nuna yadda wasu tsare-tsare da ke shimfide a bangaren samun ƴancin tafi da harkokin addinai da ke haifar da takura ga 'yancin gudanar da lamuran addini tsakanin al’umma a Najeriya.

A yayin da ta kara da cewa a halin yanzu akwai jihohi da dama a kasar da ke aiwatar da dokokin ɓatanci ga addini wajen gurfanar da mabiya addinai da suka hada da kiristoci da musulmi da kuma wasu mabiya addinan tare da zartas da hukunci a kansu.

A cikin rahoton ta na Shekara-shekara na 2024, hukumar ta ce, Gwamnatin kasar ta kuma ci gaba da kawar da kai a kan ayyukan ta’addanci da kungiyoyin ƴan ta’adda, irin su ISWAP, da Boko Haram, da sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke yi akasar.

Hukumar ta USCIRF ta ci gaba da cewa, wannan tashin hankalin babu wanda ya bari domin yana shafar ɗimbin kiristoci da Musulmai a jihohi, saboda babu inda suka keɓe wajen kai hare-hare, tare da kira ga gwamnatin Najeriya na ganin ta tashi tsaye a kokarin ta na shawo kan matsalar, wacce taƙi ci taƙi cinyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)