Amurka na bincike kan yadda ake sarrafa kuɗaɗen tallafin da ta ke badawa

Amurka na bincike kan yadda ake sarrafa kuɗaɗen tallafin da ta ke badawa

A sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar, ya kuma yi alawadai da irin ayyukan ta’addancin da ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ƴanta’adda ke gudanarwa a ƙasar, inda ta jaddada aniyarta na yin aiki tare da Najeriya da sauran abokan hulɗarta da ke yankin yammacin Afrika, don yaƙi da ta'addanci.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, tun a ranar 14 ga watan Nuwambar shekarar 2013 ne a hukumance, Amurka ta ayyana Boko Haram a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Wannan dai ya biyo bayan matakin da shugaban Amurkan Donald Trump ya ɗauka a watan Janairun daya gabata, na dakatar da duk wani tallafin da ƙasar ke bai wa ƙasashe har na tsawon kwanaki 90, don samun damar gudanar da bincike kan irin ruɗanin da ake samu wajen sarrafa kuɗaɗen da ta ke fitar wa da sunan tallafi.

A ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne dai, ɗan majalisar dokokin Amurka Scott Perry ya yi iƙirarin cewa, ana ƙarƙatar da kuɗaɗen da ƙasar ke warewa na tallafi wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a wasu ƙasashe.

Bayan wancan zargi ne dai, Sanata Ali Ndume ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike, kuma tuni majalisar dattawar Najeriya ta gayyato mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro da hafsan tsaron ƙasar da shugaban hukumar DSS don yi mata bayani kan sahihancin wancan zargi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)