Zanga-zangar da ta gudana daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ta rikide zuwa tarzoma a wasu sassan ƙasar, inda aka samu rahotanni sace-sace a da lalata kadarori a wasu jihohi da damma.
Amnesty ta zargi mahukuntan Najeriya da yin amfaani da ƙarfi a kan masu zanga-zangar lumana, inda ta ce ko a jiya Juma’aa, sai aaka gurfanar da sama da mutane 400 a gaban ƙuliya.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, Amnesty ta bayyana gurfanar da sama da mutane ɗari 4 da mahukuntan Najeriya suka yi a jihar Kano a matsayin rashin adalci, kana ta buƙaci a saki waɗanda aka garƙame a gidajen yari na sassan ƙasar ba tare da bata lokaci ba.
Amnesty ta kuma buƙaci gwamnati ta kare hakkin al’ummar ƙasar da kuma mutunta damarsu ta nuna amincewa ko akasi a kan duk wai abin da ya shafe su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI