Gwamnan jihar Farsefa Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ga manema labarai, yayin da yake raba ƙuɗaɗe da dafaffen abinci ga mutane da suka nemi mafaka a sansanin ƴan gudun hijirar Bakassi da ke Maiduguri wannan Laraba.
Gwamna Zulum ya ce an kafa kwamitin agajin gaggawa domin dakile barkewar cututtka masu nasaba da ambaliyar ruwa a Maiduguri fadar gwamnatin jihar da Jere.
Hukumar agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon iftil’in da ya auku cikin daren Talata.
Kawu yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, sai dai NEMA ta ce wasu mutane ciki harda ƙananan yara sun bace.
Tunbatsar madatsar ruwa ta Alau da ke kilomita 10 daga wajen birnin ne ya malala ruwa cikin gari, tare da lalata kadarori da dama da suka hada da, gidaje, gonaki da wuraren kasuwanci.
Cikin wuraren da lamarin ya shafa harda bababar Kasuwar Maiduguri Monday Merket, da fadar Shehun Borno, da babban asibitin koyarwa, da gidan gyran hali na New Prison.
Angunani da lamrin ya shafa wanda akasarinsu na cikin ƙaramar hukumar Jere, sun hada da Shehuri da Gwange da Adamkolo da Gamboru da Fori da Bulabulin da Post Ofice da Moromoro da kwastam.
Mazunan wadannan anguwanni sun ce har yanzu suna ci gaba da neman wasu ƴan uwansu da suka bace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI