Ambaliyar ruwa ta tono ƙaburbura a Kaduna

Ambaliyar ruwa ta tono ƙaburbura a Kaduna

Lamarin ya faru ne a unguwar Chikaji da ke Ƙaramar Hukumar Sabongari, yayin da jama'ar unguwar suka mika kokensu ga gwamnati suna rokon ta da ta gina musu magudanan ruwa don dakile sake aukuwar ibtila'in nan gaba.

A yayin zanta wa da manema labarai, Dagacin Chikaji, Alhaji Auwal Sani-Danbaba ya bayyana cewa, ambaliyar ta kuma shafi sama da gidaje 200 a yankin.

Dagacin ya kara da cewa, a halin yanzu, da dama daga cikin ƙaburburan na nan a buɗe a maƙabartar ta Hayin Ojo.

Sai dai babu wani rahoto dangane da samun asarar rai ko kuma mummunar jikkata, yayin da mazauna yankin ke cewa, babu wata hukuma ko kuma jami'an gwamnati da suka kawo musu ɗauki a lokaci da kuma bayan aukuwar ambaliyar ruwan.

Babban Limamin Chikaji, Sulaiman Liman ya bayyana cewa, sun kira taron gaggawa da mawadatan wannan unguwa domin tattaunawa da su kan yadda za a tinkari wannan ibtila'in tare da agaza wa waɗanda lamarin ya shafa da suka haɗa da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)