Ambaliyar ruwa ta raba dubban mutane da muhallansu a Jigawa

Ambaliyar ruwa ta raba dubban mutane da muhallansu a Jigawa

Rahoton ya ƙara da cewar, baya ga waɗanda aka rasa, aƙalla mutane dubu  9,366 ambaliyar ta raba da muhallansu, bayan rusawa ko mamaye gidajen da aka ƙiyasta yawansu ya kai dubu 4,699, sai kuma gonaki sama da dubu guda da suka salwanta.

Yayin da yake ƙarin haske kan halin da ake ciki, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Jigawa Dakta Haruna Mairiga ya ce gwamnati a matakin jihar ta fara tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa ta hanyar raba musu kayan abinci da  magunguna a wuraren da suke samun mafaka da suka haɗa da wasu makarantun firamare.

Wani yanki a Jihar Jigawa da Ambaliyar Ruwa ta mamaye. 26, Satumba, 2020. Wani yanki a Jihar Jigawa da Ambaliyar Ruwa ta mamaye. 26, Satumba, 2020. AP - Sani Maikatanga

Bayanai sun ce a halin yanzu ambaliyar da ta afkawa sassan Jihar Jigawa, ta yi wa garuruwa ko yankuna aƙalla 90 ɓarna.

Kafin fara daminar bana Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriyar NIMET ta yi hasashen cewa za a fuskanci saukar ruwan sama kamar da  bakin ƙwarya babu ƙaƙƙautawa a aƙalla ƙananan hukumomi 18 daga  cikin 27 da ke faɗin jihar ta Jigawa.

Iftila’in ambaliyar ruwa ba sabon abu bane a jihar Jigawa, sai dai a ‘yan shekarun baya bayan nan, lamarin yayi munin da ke janyo hasarar ɗimbin rayuka, muhallai da kuma tarin gonakin da ake dogaro dasu wajen samar da wadatar abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)