A Alhamis ɗin nan ne Hukumar NEMA ta bayyana halin da ake ciki game da irin ta’adin da ambaliyar ruwan ta haifar a sassan ƙasar, inda ta ce akalla kadada dubu 107,652 ta shafe, ta kuma lalata gidaje dubu 80,049.
Daga cikin jahohin da iftila’in ya shafa akwai jihar Ribas da Neja da Benue da kuma jahohin da dama da ke ke yankin arewacin ƙasar.
Akalla ƙananan hukumomi 137 daga jahohi 28 ne ambaliyar bana ta shafa kamar yadda hukumar ta bayyana.
A ziyarar da kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya kai ofishin NEMA, Darekta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta ce NEMA ta gudanar da bincike a kusan dukannin jahohin ƙasar dangane da iftila’in, sannan ta ƙara da cewa rashin samun tallafin kuɗi ne babbar matsalar da ke shafar aikin hukumar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI