Al'ummar Maiduguri na zaman ɗar-ɗar bayan tserewar fursunoni da namun daji a Ambaliya

Al'ummar Maiduguri na zaman ɗar-ɗar bayan tserewar fursunoni da namun daji a Ambaliya

Ambaliyar wadda bayanai ke nuna cewa ita ce mafi muni da birnin Maiduguri ya fama da ita cikin shekaru 30 da suka gabata, tuni ya raba kusan rabin al'ummar tsakar birnin da muhallansu.

Sai dai a wani yanayi da hijira baya ga fakewa a wurare marasa cikakken tsaro ya zamewa jama'a dole, yanzu haka al'ummar birnin na rayuwa ne cike da fargaba saboda tsoron abin da ka iya faruwa bayan da tarin namun daji suka sulale ta cikin ruwa a gidajen da ake ajiye da su.

Haka zalika bayanai sun ce, akwai fursunoni aƙalla 200 da suka tsere daga gidan yari bayan da ruwa ya ci kurkukun da suke tsare.

Dangane da wannan wakilinmu daga birnin Maiduguri Bilyaminu Yusuf ya haɗa mana rahoto.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken rahoton..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)