Rikicin na shekarar 2001 da ya fantsama izuwa sassa daban-daban na jihar Filato da ke tsakiyar tarayyar Najeriya ya yi sanadin mutuwar mutane masu tarin yawa musamman a ƙwaryar birnin jihar.
A wani ƙoƙari na tabbatar da fahimtar juna tsakanin musulmi da kirista da suka rayu tare a shekaru 20 da suka gabata amma rikici ya ɗaiɗaita jama’ar yankin Gangare suka haɗa wani taro da suka kira na ƴan uwantaka domin ƙara samun haɗinkai tsakanin mabiya addinan biyu.
John Gangare ya ce kafin faruwar wannan rikici suna rayuwa cikin lumana a wannan yanki, kuma shine malamin majami’ar ECWA a wannan yanki kafin rikicin ya tirsasa masa barin garin.
Ya ce ya ji daɗi matuƙa da wanann haɗuwa da suka yi domin cimma burin dawo da ƴan uwantaka da ke tsakaninsu.
Shima Malam Aliyu Aliyu wanda shine limamin Masallacin Gangare ya ce a wannan rana da suka haɗu tana da matuƙar muhimmanci domin suna da nufin dawo da ƴan uwantaka da ke tsakaninsu shekaru aru-aru.
Ya kwatanta abin da ya faru a shekarar 2001 a matsayin son rai, domin addinin musulunci bai koyar da cewar mutum ya yaƙi maƙocinsa ba saboda banbancin addinin.
Dukda faruwar kashe-kashe tsakakaninsu sama da shekaru 20 da suka gabata amma al’ummar yankin Gangare na da yakinin cewa wannan haɗuwa da suka yi zata sake buɗe kofar zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI