Al'umar jihar Zamfara a Najeriya sun koka akan yadda 'yan ta'adda ke cin karesu ba babbaka

Al'umar jihar Zamfara a Najeriya sun koka akan yadda 'yan ta'adda ke cin karesu ba babbaka

koken na Al'umar Zamfara na zuwa ne a daidai liokacin da Manyan hafsoshin sojin Najeriya da suka yi ritaya suka bayyana damuwarsu kan yadda hare-haren ta’addanci suka sake kunno kai a yankin Arewa-maso-Gabas, inda suka jaddada bukatar ganin an ɗauki ƙwararan matakan daƙile hare-haren cikin gaggawa.

Sai dai ƙungiyar Amnesty International ta yi nuni da cewa ta'addancin na nuni da gazawar matakan tsaro ne da ake ɗauka a yanzu.

A baya bayan nan rahotanni sun nuna cewa an kashe akalla manoma 40 a kauyen Dumba da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno a ranar Lahadin da ta gabata, sakamakon wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne da mayakan kungiyar IS da ke yankin yammacin Afirka.

Sannan kuma a ranar Talata mayakan Boko Haram suka kai hari a unguwar Shikarkir da ke karamar hukumar Chibok a wannan jihar, inda suka kona majami’a guda da wasu gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)