Allon tallata takarar Tinubu na zaɓen 2027 ya bayyana a Abuja

Wannan allon tallata Tiubu da aka kafa a unguwar Area One da ke babban birnin tarayya Abuja ya jawon cece-kuce, tsakanin ƴan anguwar da sauran masu bin hanyar.

A jikin allon wanda ke ɗauke da hoton shugaban ƙasa da mai ɗakinsa, an rubuta kalamun nuna “Goyan baya ga Tinubu a zaɓen 2027.

Babu sanarwa a hukunce

Kawo yanzu dai shugaban ƙasar Bola Tinubu bai yi wata sanarwa a hukumance ba game da tsayawa takara na neman wa’adi na biyu.

Tinubu ya ɗare karagar mulkin Najeriya ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, sakamakon nasarar da ya yi a babban zaɓen ƙasar, inda ya cika burinsa na zama shugaban ƙasa.

Tsadar rayuwa

Tun bayan hawansa mulki watanni 16 da suka gabata, ƴan Najeriya sun shiga cikin wani yanayi na halin ƙunci sakamakon sanar da janye tallafin man fetir da ya yi a ranar farko ta soma mulkinsa, tare da karya darajar Naira.

Masana sun danganta waɗannan manufofinsa da ummul a ba’isin wahalhalun tattalin arziƙi da al’umma shuka shiga.

Bacin rai ya kai ga zanga-zangar da aka yi wa lakabi da #EndBadGovernance da ta gudana a fadin ƙasar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)