Akwai yuwuwar ƙara kuɗin kira da na data a sabuwar shekarar 2025 a Najeriya

Akwai yuwuwar ƙara kuɗin kira da na data a sabuwar shekarar 2025 a Najeriya

Wani babban jami’i da ya nemi a sakaya sunanshi ya ce hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ka iya bai wa kamfanonin damar ƙara kuɗi.

Dailytrust ta rawaito cewa dukda tsadar rayuwa ammaanƙi amincewa kamfanonin su ƙara kuɗin kira sama da shekaru 11 da suka gabata.

Kamfanoni kamar MTN da Airtel da 9Mobile sun jima suna miƙa buƙatar ƙarin kuɗin GA Hukumar duba da yanayin tattalin arziki a ƙasar.

Wasu majiyoyin kamfanonin sadarwar sun ce ƙarin da za a fuskanta a ƙasar zai iya kaiwa kaso 40.

Wannan na nufin cewa kiran waya na minti 1 zai tashi daga naira 11 zuwa 15.40, aika sakon kar ta kwana a salula zai tashi daga naira 4 zuwa naira 5.60.

Farashin data 1GB zai tashi daga naira dubu 1 zuwa dubu1 da 400

A ranar 20 ga watan disamba a wata tattaunawa da manema labarai ministan sadarwa na Najeriya Dr. Bosun Tijani ya nuna cewar akwai buƙatar sake duba farashin.

A shekarar 2023 ne kamfanin MTN yayi asarar da ta kai Naira biliyan 137, asarar da ta ƙaru zuwa biliyan 514.9 a watanni 9 na farkon 2024.

Kamfanin Airtel dake aiki a Afrika shima ya sanar da yin asarar da ta kai dala miliyan 89 a 2024 kuma hakan ya biyo ƙaluabalen da yake fuskanta a Najeriya

Kawo lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin da abin ya shafa a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)