Akpabio na azabtar da ni saboda na ƙi amincewa ya yi lalata da ni - Sanata Natasha

Akpabio na azabtar da ni saboda na ƙi amincewa ya yi lalata da ni - Sanata Natasha

Sanata Natasha ta bayyana haka a wata hira da ta yi da kafar talabijin ta Arise a yau Juma'a, hirar da ke zuwa bayan tankiyar da aka samu tsakaninta da Akpabio a makon jiya a yayin da Majalisar Dattawan da ke gudanar da zamanta, batun da tuni ya karaɗe kafafen yaɗa labarai a cikin Najeriya.

Tankiyar ta makon jiya, ta samo asali bayan sanata Natasha ta yi korafi kan yadda aka sauya mata kujerar zamanta a zauren majalisar ba tare da izininta ba, abin da ya sa ta yi musayar yawu da shugaban majalisar

Tuni Majalisar Dattawan ta mika sanata Natasha ga Kwamitin Ɗa'a na majalisar domin ladabtar da ita.

An bai wa kwamitin, ƙarƙashin jagorancin sanata Neda Imaseun, wa'adin makwanni biyu da ya gabatar da rahotonsa kan sanata Natasha.

Sanata Natasha dai ta shigar da karar Akpabio, tana neman ya biya ta diyyar sama da Naira biliyan 100, yayin da ta ce tana da hujjojin da ta tattara a kan shugaban majalisar.

Natasha ta ce, tana da kwafin zancen da suka yi da Akpabio ta manhajar WhatsApp, yayin da ta buƙaci Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS da ta banƙado zancen da suka yi.

Tankiyata da Akpabio ta soma ne a ranar 8 ga watan Disamban 2023, lokacin da muka ziyarci jihar Akwa-Ibom tare da mijina domin halartar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Akpabio. Akpabio ya rike hannuna yana ta nuna min sassan gidansa duk da cewa, mijina na biye da mu a baya. Ya nemi na rika zuwa gidansa domin gudanar da hutu na musamman a cikinsa. Mijina ya saurari kalamansa, inda ya faɗa min cewa, kada na kuskura na yi balaguro zuwa ƙasar waje ni kaɗai ko kuma tare da shugaban majalisar.

Kazalika sanata Natasha ta zargi Akapbio da dakile kudirin da ta gabatar a zauren majalisar na neman a gudanar da bincike kan bakaɗalar cin hancin da aka tafka a masana'antar sarrafa ƙarafa ta Ajaokuta, inda ta ce, shugaban majalisar ya nemi yin lalata da ita kafin amincewa da kudirin nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)