Akalla mutane 100 ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a Jigawa

Akalla mutane 100 ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce akasarin wadanda abin ya rutsa da su sun mutu ne sakamakon kewaye wurin da al’amarin ya faru duk da kokarin da ƴan sandan suka yi wajen kawar da su inda tankar ke cin wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Shi’isu Adam, ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Talata a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura.

Da yake magana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN yau Laraba, Adam ya kuma ce an kwantar da wasu mutane 50 a asibiti sakamakon raunuka daban-daban sakamakon ƙunar da suka samu a sanadin gobarar.

Kakakin ya kara da cewa “Da misalin karfe 11:30 na dare na ranar Talatar da ta gabata ifitila’in ya faru a kusa da jami’ar Khadija, dake garin Majia a karamar hukumar Taura a jihar Jigawa tankar ta yi bindiga ta kuma kama wuta nan take.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara dacewa "Direban ya baro Kano ne inda ya nufi garin Nguru na jihar Yobe lokacin da hatsarin ya afku.

Jami’in ya ci gaba da cewa “Muna cikin damuwa cewa duk da gargadin da ‘yan sanda suka yi na cewa mutane su nisanta kansu daga wuraren hadurran da suka shafi tankokin mai, amma har yanzu ba sa yin abin da ya kamata.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata na samun kulawa a babban asibitin Ringim.

Daruruwan mutane ne suka mutu sakamakon hadurran tankokin mai a sassa daban-daban na Najeriya.

A wasu lokuta, akasarin wadanda abin ke rutsawa da su, mutane ne da ke taruwa a kusa da motar dakon man domin dibar mai daga cikin tankar kafin wani mummunan abu ya afku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)