Afenifere ta caccaki Tinubu a kan jawabinsa ga ƴan Najeriya

Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Justice Fakiyesi ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai bayan jawabin da Tinubu ya gabatar ga ƴan Najeriya a kan zangar-zangar tsadar rayuwa, kinda ya ce abin takaici ne gannin yadda shugaban ya zaƙe a kan manufofin da ke musguna wa al’umma ta wajen ci gaba da janye tallafin mai.

A cewarsa, jawabin shugaban bai taɓo batun matsalar yunwa da ƴan Najeriya ke kokawa a kai ba, yana mai cewa kira da ya yi don tattaunawa ba zai sauya komai .

 

Ya ce manufofin tattalin arzikinsa na jari-hujja babbar matsala ce, kuma ci gaba da aiwatar da su ya nuna rashin jinkan al’umma, kuma babu tsammanin zai sauya.

 

Kakakin na Afenifere ya ce Tinubu ya yi rashhin azanci wajen bayyana zanga-zangar a matsayin wadda aka shirya don wani dalili na siyasa, duk da cewa shi ma ya yi kira a yi wa gwamnatin  tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan zanga-zanga da bore.

 

Shi ma da ya ke tsokaci, wata jigo a ƙungiyar Afenifere, kuma tsohuwar mataaimakiyar gwamnan   jihar Lagos, Kofoworola Bucknor Akerele,  ta ce jawabin na Tinubu abin takaici ne.

Ta ce bai taɓo batun da ake zanga-zanga a kai ba, musamman ma na tsaro, wanda rashin sa ya hana ɗimbim manoma zuwa gonakinsu, lamarin da ya ta’azzara ƙarancin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)