Chidimma mai shekaru 23, wanda maahaifinta haifaffen Najeriya ne, kuma mahaifiyarta ƴar ƙasar Afrika ta Kudu ce, kuma bayan fitowarta a gasar Sarauniyar kyau ta ƙasar, ƴan Afrika ta Kudu, ciki har da wata ministar gwamnati suka nuna adawa da shigar ta saboda tushenta, lamarin da ya sa ta janye daga baya.
Tana janyewa daga Afrika ta Kudu ne aka shawarce ta ta koma Najeriya, ƙasarta ta asali, shawarar da ta yi aiki da ita, ta kuma samu biyan buƙata.
Bayan nasarar da ta samu, Chidimma ta bayyana jin daɗinta da irin alfaharin da ta ke da shi a game da samun damar wakiltar Najeriya a babbar gasar fidda sarauniyar kyau.
Ta kara da cewa ƴan Najeriya da ke zaune tare da yiun kasuwanci a Afrika ta Kudu na fuskantar tashin hankali da hare -hare daga ƴan ƙasar a wasu lokuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI