Adeshina ya ce a shirye yake ya yiwa Nijeriya aiki a kowanne matsayi

Adeshina ya ce a shirye yake ya yiwa Nijeriya aiki a kowanne matsayi

Adeshina wanda ya riƙe muƙamin ministan noman Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Goodluck Jonathan daga shekarar 2010 zuwa 2015 ya zama shugaban Bankin Afirka ne a shekarar 2014.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Tsohon ministan ya ce a shirye yake ya bada gudummawa ta kowanne fani domin ciyar da Nijeriya gaba, ko da kuwa a matsayin shugaban kasa ne.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da Akinwumi Adeshina bayan samun nasarar zama shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da Akinwumi Adeshina bayan samun nasarar zama shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka Bashir

Adeshina ya taka rawa sosai wajen bunƙasa bangaren noma a matsayin minista, ya yin da kuma tagomashinsa ta ƙara haske da ya karbi ragamar jagorancin Bankin Raya Ƙasashen Afirka inda ya yi aiki na shekaru 10

Mutane da dama na kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin ƙwararrun mutanen da suka fito daga Afirka kuma masu hazaƙar da ka iya kawo sauyi wajen shugabancin Nijeriya mai dauke da ɗimbin matsaloli.

Ikrarinsa na shirin bada gudumawar ta samu goyan bayan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƴan siyasar  arewacin Nijeriya ta LND wadda tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranci.

Shekarau na daga cikin waɗanda suka bukaci Adeshina da ya koma gida domin bada tasa gudumawar bayan kammala wa'adinsa a Bankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)