Wannan ya sa aka samu karuwar kashi 7 cikin 100 na ƙaruwar adadin takaddun kudin da ke hannun al’umma daga wata ɗaya da ya wuce.
Yawan takaddun naira da ke hannun ƴan ƙasar a yanzu ya kai naira tiriliyan 4.8
Wannan na ƙunshe a bayanan da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar, inda ya nuna cewar an samu karancin takaddun kuɗi hatta a bankunan ƙasar inda ya ƙaru daga tiriliyan 4.2 zuwa tiriliyan 4.6.
Alkaluma sun nuna cewa adadin takaddun kuɗin da ya ƙaru a hannun jama’a a wannan shekara mai ƙarewa ya kai sama da tiriliyan 1 wanda ya ƙaru a kan sama da naira tiriliyan 3.6.
A baya-bayannan ana fuskantar ƙarancin takaddun kuɗi a Najeriya abin da ya sa aka ƙayyade adadin kuɗin da ƴan kasar za su na cirewa a na’urar ATM.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI