Mahukuntan jihar sun ce zuwa yanzu an tattara gawarwakin mutane 30 yayinda NEMA ke ci gaba da aikin laluben waɗanda suka maƙale a saman rufin gidaje da wurare masu haɗari.
Hukumar NEMA ta ce ambaliyar ta shafi mutane miliyan 1 da rabi waɗanda ke halin tsananin buƙatar agaji, musamman ganin yadda suka bar muhallansu a yanayi na ɗimuwa sakamakon mummunar ambaliyar wadda ta faro da tsakaddaren Talata.
Kakakin hukumar ta NEMA Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kawo yanzu mutane 30 suka tabbatar da mutuwarsu ko da ya ke alƙaluman ka iya ƙaruwa sakamakon yadda har yanzu aka gaza gano mutane da dama da suka bace a ruwan.
Tun farko ɓallewar madatsar ruwa ta Alau ita ta haddasa tumbatsar ruwa a tituna da magudanan Maiduguri wanda zuwa yanzu ya lalata tarin kadarorin da ba a kai ga ƙiyasin ƙudinsu ba, baya ga ginaku da gidajen jama’a da kuma wuraren kasuwanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI