Adadin man fetur da ƴan Najeriya ke sha kowacce rana ya ragu da kashi 92

Adadin man fetur da ƴan Najeriya ke sha kowacce rana ya ragu da kashi 92

Alƙaluman da hukumar kula da albarkatun ruwa da kuma ƙarƙashin ƙasa da gidan Talabijin na Channels a Najeriya ya samu sun nuna cewar ana shan lita miliyan 4 da dubu 500 a kowacce rana a ƙasar a 20 ga watan Agustan 2024.

To sai dai a watan Mayu a kowacce rana ana shan lita miliyan 60. Wannan ne ya nuna cewar an samu raguwar ainin kan man da ake sha kuma ya ragu da kashi 92 cikin 100.

Bayanan wannan hukuma sun nuna cewa a cikin jihohi 36 guda 16 ne suka karbi mai daga kamfanin NNPCL wannan wata. Hakan na nuna cewar duk jihohin da basu karbi mai daga kamfanin ba sun fuskanci ƙarancinsa sosai.

Bayanai sun nuna cewar jihar Niger ce ta fi samun mai da yawa inda aka kai mata mota 21 kimanin lita dubu 940 sai Lagos ta karbi mota 12 sama da lita dubu 726, jihar Kaduna an kai mata  mota 12 dauke da sama da lita dubu 454.

Sauran jihohin da suka samu adadi mafi yawa sune  Oyo inda aka kai mata mota 12 dauke da lita dubu 454 sai Kano aka kai mota 9, Kwara mota 6, Edo mota 4 sai birnin tarayya Abuja mota 4.  

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu 2023, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Shugaban ya ce biyan tallafi ba abune mai ɗorewa ba kuma ya jefa ƙasar cikin kangin cin bashi.

Wannan mataki ya sa farashin man fetur ya tashi daga Naira 195 zuwa kusan 1300 kan kowacce lita, abinda ya ƙara ta’azzara tsadar rayuwa da tashin farashin kayan masarufi a ƙasar.

Tsadar rayuwar ta kuma jefa mutane miliyan 129 cikin matsanancin talauci kamar yadda alƙaluman bankin duniya sunka tabbbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)