Adadin ƴan Najeriya da ke ƙarƙashin shirin inshorar lafiya ya haura miliyan 19

Adadin ƴan Najeriya da ke ƙarƙashin shirin inshorar lafiya ya haura miliyan 19

Babban daraktan hukumar ta NHIA Kelechi Ohiri yayin jawabin da ya gabatar gaban zaman taron kwana guda na masu ruwa da tsaki a lamurran na Inshorar lafiya, ya bayyana samun gagarumin ci gaba a tafiyar ko da ya ke ya bayyana cewa akwai tarin ƙalubale wajen shawo kan jama’a game da muhimmancin tsarin.

A cewar Mr Ohiri fatan hukumar shi ne ganin aƙalla kashi 70 na ƴan Najeriya sun rungumi tsarin na Inshorar lafiya zuwa nan da 2027, lura da yadda ƙasar ke sahun baya a wannan tsari.

Najeriya na sahun ƙasashen da aka bari a baya ta fuskar inshorar lafiya inda kaso mai yawa na aal’ummarta ke rayuwa ba tare da inshorar ba, lamarin da ke jefa jama’a a wahala yayin rashin lafiya.

Babban daraktan ya bayyana cewa abin alfahari ne samun mutane miliyan 19 da dubu 200 ƙarƙashin tsarin na Inshora adadin da ya ce ya matuƙar ƙaruwa a baya-bayan nan sakamakon wayar da kai.

A cewar Mr Ohiri sabon gangaminsu zai faro daga 2025 zuwa 2027 a ƙoƙarin sake janyo hankalin jama’a don shiga tsarin na Inshorar lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)