Abba ya ba da umarnin bincike kan rage wa ma’aikatan Kano albashi

Abba ya ba da umarnin bincike kan rage wa ma’aikatan Kano albashi

Hakazalika ya ce a yi bincike kan rashin biyan wasu ma’aikatan albashinsu.

Ya bayyana lamarin a matsayin cin zarafin ma’aikata da tauye musu haƙƙi.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ma’aikatan sun shafe watanni ba tare da karɓar cikakken albashinsu ba.

Gwamna Abba ya sha alwashin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da hukunta su.

“Wannan gwamnati ba za ta amince da zaluntar ma’aikata ba.

“Duk wanda aka samu da hannu a wannan laifi zai fuskanci hukunci,” in ji shi.

Don shawo kan matsalar, gwamnan ya kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai ƙarƙashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, Kwamishinan Kula da Ci Gaban Karkara wanda kuma shi ne tsohon Akanta-Janar na Jihar.

Akwai ƙwararru a harkar kuɗi da manyan jami’an gwamnati a cikin kwamitin, waɗanda za su duba takardun albashi daga watan Oktoban 2024 zuwa Fabrairun 2025.

Ayyukan kwamitin sun haɗa da gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance asarar kuɗi da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a magance matsalar gaba ɗaya.

Gwamnan ya bai wa kwamitin wa’adin kwana bakwai don kammala bincikensa da kuma miƙa rahoton.

Gwamna Abba ya tabbatar wa ma’aikatan jihar cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da adalci da kuma biyan albashi a kan lokaci a nan gaba.

Ya gargaɗi duk wanda aka samu da laifin yin almundahana da albashin ma’aikata cewa ba za a kyale shi ba.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne, ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)