Abacha ne ya jagoranci rusa zaben Abiola – Babangida

Abacha ne ya jagoranci rusa zaben Abiola – Babangida

A cikin littafin tarihinsa da ya rubuta kuma aka ƙaddamar yau Alhamis, Babangida ya bayyana cewa yana Katsina domin ta'aziyar Alhaji Musa 'yar Adua, mahaifin Janar Shehu 'yar Adua da kuma tsohon shugaban ƙasa Umaru 'yar Adua mai magana da yawun mataimakinsa ya sanar da rusa zaben da attajiri MKO Abiola ya lashe, a ƙarƙashin Jam'iyyar SDP.

Tsohon ɗan takara shugabancin ƙasa a Najeriya, MKO Abiola kenan. Tsohon ɗan takara shugabancin ƙasa a Najeriya, MKO Abiola kenan. © Premiumtimes

Babangida yace daga baya ne ya gano cewar tsohon shugaban ƙasa Janar Abacha ne wanda a lokacin mulkinsa yake riƙe da mukamin Ɓabban Hafsan tsaron ƙasa ya jagoranci masu adawa da zaben.

Taƙaddamar da ta biyo bayan zaben ta sanya Babangida sauka daga mulki a watan Agustan shekarar 1993, tare da dora gwamnatin riƙon kwarya a ƙarƙashin Ernest Shonekan, wadda Abacha ya kawar da ita a watan Nuwamba.

Janar Abacha ne ya kama Abiola ya kuma tsare shi saboda ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa.

Janar Sani Abacha daga hagu, tare da MKO Abiola. Janar Sani Abacha daga hagu, tare da MKO Abiola. © dailytrust

Tsohon shugaban ƙasar wanda ya yiwa jama'ar Najeriya jawabi a ranar 24 ga watan Yunin shekarar 1993, inda ya tabbatar da rusa zaɓen, ya bayyana cewa Abacha ya zama wani ginshiƙi na masu adawa da zaɓen da aka yi, kuma yake da magoya baya da dama a cikin manyan sojojin Najeriya.

Babangida ya yi bayani dalla dalla akan irin matsalolin da suka yiwa shirin zaɓen tarnaki kafin gudanar da shi da kuma bayan an yi shi.

Tsohon shugaban yace tun gabanin gudanar da zaben aka fara samun zagon ƙasa daga wasu marasa kishin ƙasa, cikin su harda ƙungiyar ABN wadda ke ƙarƙashin attajiri Arthur Eze, wadda ta ruga kotun Abuja a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Bassey Ikpeme, wanda ya bai wa Hukumar NEC umarnin dakatar da shirin zaben.

Wannan umarni, in ji Babangida, ya haifar da ruɗani a ciki da wajen Najeriya, abinda ya sa shi kiran taron gaggawa na majalisar tsaron ƙasa, inda ya bai wa shugaban Hukumar zaben umarnin ci gaba da shirin zaɓen duk da adawar da wasu daga cikin jiga jigan hafsoshin tsaron ƙasar, cikin su harda Janar Abacha da Joshua Dogonyaro da kuma wasu shugabannin rindinonin sojin kasar.

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha kenan. Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha kenan. © dailytrust

Tsohon shugaban ya bayyana cewar wanda ya goya masa baya a lokacin shi ne shugaban sojojin ƙasa, Janar Salihu Ibrahim.

Yayin da ake wannan, sai kuma wata kotu a Lagos ta bada wani umarnin da ya yi karo da na Lagos, inda ta bukaci hukumar zaɓe ta je tayi zaben.

Babangida yace bayan gudanar da zaben, da kuma fara gabatar da sakamako, a ranar 16 ga wata sai shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Humprey Nwosu ya sanar da dakatar da bada sakamako ba tare da saninsa ba, kuma daga nan ya gano cewar akwai wasu fitattun mutanen dake adawa da zaben, kuma ya dace ya yi taka tsantsan.

Daga ƙarshe Babangida ya ɗauki alhakin rusa zaben da kuma duk wasu kura kuran da aka samu a gwamnatinsa, ya yin da ya nemi gafarar 'yan Najeriya akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)