Aƙalla manoma dubu 500 rikici ya tilastawa barin muhallansu a Najeriya - Masana

Aƙalla manoma dubu 500 rikici ya tilastawa barin muhallansu a Najeriya - Masana

A taron shekara -shekara  karo na ashirin da bakwai  na kungiyar tsofaffin daliban jami'ar aikin gona ta gwamnatin tarayya Najeriya da ke garin Abeokuta a jihar Ogun , shugaban kungiyar Dr gbenga Olawepo Hashim ya bayyana cewar tsakanin shekarar 2022 zuwa  2024 manoman sunyi asarar kayayyakin noma na kudi fiye da Naira triliyan 2.

Bugu da kari , a yankin tsakiyar ƙasar kaɗai an samu raguwar aiyukan manoma  da kashi 70 bisa 100, wanda ya haifar da ƙarancin kayan abinci kamar masara, doya da sauransu. baya ga garkuwa da manoma aƙalla 3500 a shekarar 2024 kamar yadda cibiyar nazarin zaman lafiya ta sanar a binciken da ta gudanar.

Dr Olawepo ya ce baya ga waɗannan ƙalubalen da manoma ke fuskanta akwai wasu batutuwa kamar rashin kayayyakin aiki na zamani ,rashin kyawun hanyoyin sufuri, haɗi da asarar amfanin gona bayan girbi da ƙaranci wuraren adana kayayyakin da dai sauransu.

Daga bisani, Olawepo ya yi kira  ga manoma a faɗin ƙasar da su haɗa kai wajen  shawo kan matsalar da ake fuskanta a aikin noma a ƙasar, a gefe guda ita ma gwamnati sai ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin shawo kan matsalolin noma da ke haddasa ƙarancin abinci da tsadarsa a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)