Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 da rabi na daren jiya Talata, kuma mafi yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su mata ne da ƙananan yara da suka taso daga garin Mundi.
Majiyoyi daga yankin da abin ya faru, sun ce al’ummar yankin sun yi gaggawar kai dauƙi, inda aka samu nasarar kuɓutar da wasu da ransu.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Neja Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya ce an samu nasarar kuɓutar da mutane 150, sannan kuma ana ci gaba da laluben waɗanda suka ɓace.
Ya ce jami'an Hukumar ta NSEMA ɓangaren kai ɗaukin gaggawa da hadin gwiwar Ma’aikatar Sifuri ta jihar da kwamitin kai ɗaukin gaggawa na ƙaramar hukumar Mokwa da masinta, sun duƙufa wajen aikin laluɓen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI