Sabuwar kwayar cutar coronavirus ta kasance wata annobar da ta kada zuciyar duniya. Wannan kada zuciyar ta fita shafuwar Amurka. Wasu na ganin cewa wacannan ita ce mafi girman fitina da duniya ta fuskanta tun bayan yaķin duniya na biyu.
Wannan sharhin Dkt.Murat Yeşiltaş ne daraktan harkokin tsaron a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Halayyar Dan Adam watau SETA...
Annobar ta sanya attaunawa akan yadda tsarin duniya zata sake kasancewa sake kunnu kai a farfajiyar masana ilimin siyasa. Wasu na hasashen cewa annobar zata sanya China ta kasance kasa mafi karfi a doron kasa; wasu kuma na ganin zata kaďa teburin jagorancin duniya da Amurka ke yi. Haka kuma a yayinda wasu ke hasashen cewa annobar zata zata kawo karshen allehiyar duniya; wasu na fatan zata haifar da haďin gwiwar ķarfafa shirin allehiyar duniya. Hasashen da bai iyakance akan wadannan kawai ba. Ana kuma sharhin cewa annobar zata karfafa ra'ayin son kasa, rage kwarin tattalin arziki da kuma haifar da canjin gwamnati a wasu ķasashe.
Da alama hakan ba zai yiwu ba idan har siyasar duniya ba ta aminta daga dukkanin wadannan canjin yanayin ba. A sabili da haka bayyana cewar corona zata iya canja tsarin duniya abu ne muyar gaske. Wacannan matsalar ba wacce zata sauya jagorancin ikon duniya bace, matsalace wacce ta bulla take kalubalantar dukkan duniya kuma zata cigaba da hakan. Ga dukkan alamu zata kara kalubalantar dukkan duniya. A sabili da hakan bayan kawo karshenta ba China ba Amurka ba babu wata kasar da zata to sanadiyar karawa karfi. A sabanin hakan annobar zata ragewa dukkan kasashen biyu karfi ta sake fitar da wata fatar da zata samar da daidaito a duniya. Haka kuma zata sauya kalubalantar ta sigar kasuwanci da iyaka da Amu8da China is yiwa juna ta haifar da wata tsari na daban.
Wannan dai lamari ne da zai rage kwarin gwiwar tattalin arziki kuma farfadowar tattalin arzikin zai ta'alaka ne ga iya lokacin da annobar zata kawo karshe. A gefe guda kuma zata gasganta rashin jituwa da juna tsakanin Amurka da China ta kuma sanya Amurka daukar matakan nazari a maimakon na karfi da karfi. A yankunan Asia Pacific rikice rikice zasu iya kara kamari domin Amurka zata iya janyewa daga lamurkan yankin.
Haka kuma kasancewar ita ma China is iya daukar iron salon Amurka a yankin Asia Pacific yankin zai kara fadawa cikin halin rashin tabbas. Hakan is iya kawo karshen fafutukan mallakar yanki da ķasashe ke yi a tsakaninsu.
Tsananta gwagwarmaya tsakanin Amurka da China lamari ne da zai iya dagula lamurkan wasu yankuna. A saboda wannan dalili, za'a iya fuskantar canji a yankin Tarayyar Turai, dangantakar Trans-Atlantic, Gabas ta Tsakiya da Kudancin Asia. Duk da haka wannan bai isa ya haifar da sauyi a tsarin jagorancin duniya ba.
Akan yadda corona zata canja duniya da kuma yadda Amurka zata kasance, dangane ga alkaluman da suka bayyana a ýan kwanakin tasiri da karfin Amurka zai rago a doron kasa.
Sanadiyar tasirin corona, sabuwar tubalin siyasa na kafuwa a doron kasa, Ayayinda a Amurka ake gudanar da zanga-zangar nuna wariyar launin fata, hakan ka iya faruwa ta kuma bazu zuwa wasu yankuna saboda wasu dalilai.
Wannan sharhin Dkt Murat Yesiltas ne daraktan harkokin tsaron a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Halayyar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.