Zimbabwe ta samu rasa rayuka mafi yawa sanadiyar Korona

Zimbabwe ta samu rasa rayuka mafi yawa sanadiyar Korona

A cikin awanni 24 da suka gabata kasar Zimbabwe ta yi rajistar mutuwar mutane 86 sakamakon kamuwa da COVID-19 mafi yawa a cikin kwana guda tun farkon annobar.

Tare da karin mutane 2,491 dauke da cutar, yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum dubu 78,872, da kuma 2,418 wadanda suka rasa rayukansu, in ji Maikatar Lafiya.

Kasar dake kudancin Afirka  ta shiga mataki  ta biyu na annobar tsakanin Janairu zuwa Maris, kuma ta uku tana gudana a halin yanzu.

Shugaba Emmerson Mnangagwa ya tsawaita dokar hana fita waje a duk fadin kasar da karin kwanaki 14 a ranar Talata, ya kara jinkirta bude makarantun da za a bude a ranar 28 ga watan Yuni. A ranar 29 ga Yuni, ya gabatar da matakan kulle-kulle wadanda suka hada da dokar hana fitan dare da kuma takaita tafiye-tafiye tsakanin biranen kasar.


News Source:   ()