A cewar Zelensky Ukraine a shirye ta ke ta damƙa sojojin ga Korea ta Arewa matuƙar shugaba Kim Jong Un zai shiga tsakani wajen aiwatar da musayar fursunonin Ukraine da ke tsare a hannun Moscow.
Cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Zelensky ya bayyana cewa adadin Sojin Korea ta arewa na ci gaba da yawa a hannun Ukraine kuma ko shakka babu adadin zai ci gaba da ƙaruwa ganin cewa ana ci gaba da kamo su daga fagen daaga.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Ukraine ta sanar da kame Sojin Korea ta Arewa a yankin Kursk na Rasha karon farko da ƙasar ke sanar da kame Sojojin na Kim Jong Un a raye, ko da ya ke tace ta hallaka ɗaruruwa.
Wannan kalamai na Zelensky na zuwa a dai dai lokacin da Korea ta kudu ke cewa adadin Sojin maƙwabciyarta Korea ta Arewa da suka mutu a fagen daaga yayin taimakawa Rasha a yaƙinta da Ukraine ya zarta dubu 3.
Ukraine da ƙasashen yammacin duniya sun yi amannar cewa akwai Sojin Korea ta Arewa aƙalla dubu 11 da ke taimakawa Rasha a yaƙnta a Kiev.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI