Zelensky ya zargi Rasha da yunkurin kai hari tashoshin nukiliyarta

Zelensky ya zargi Rasha da yunkurin kai hari tashoshin nukiliyarta

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York, ya ce ya samu bayanan sirri da ke tabbatar da masa da yunkurin kai harin.

Kwanan nan na sami wani rahoton sirri mai cike da ban tsoro, akwai alama Putin na shirin kai hare-hare kan tashoshin makamashin nukiliyar mu da gine-gine, da nufin katse wutar lantarki.

Bayan kaddamar da mamayar Ukraine da Rasha ta yi a watan Fabrairun 2022, ta kwace babbar tashar nukiliyar Zaporizhzhia.

A ƴan makonnin nan kuma, Rasha ta yi ta luguden wuta kan tashoshin wutar lantarkin Ukraine, matakin da kasashen Yammaci da ita kanta Ukraine suka bayyana a matsayin yunkurin sanya ƙasar cikin wani yanayi a lokacin sanyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)