Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane dubu 597 a shekarar 2023 - WHO

Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane dubu 597 a shekarar 2023 - WHO

Sanarwar da kungiyar kawancen Gavi dake yaki da cututtuka ya gabatar, ya ce alkaluman Majalisar dinkin duniya ya nuna cewar an samu karuwar akalla mutane miliyan 11 da suka harbu da cutar daga cikin adadin da aka samu a shekarar 2022, yayin da adadin wadanda suka mutu kuma ke kankankan a tsakanin shekarun biyu.

Wani abin tada hankali shi ne yadda akasarin wadanda suka mutu, wadanda yawansu ya kai kashi 95 na alkaluman da aka gabatar, ya nuna cewar daga Afirka suka fito, abinda ya sa shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Ghebreyesus ya yi kirar daukar matakan gaggawa domin tinkarar matsalar.

Ghebreyesus yace babu dalilin da zai sa wani mutum ya mutu sakamakon wannan cutar wadda ke ci gaba da illa da kuma kassara jama'a a yankin Afirka, musamman mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Shugaban hukumar lafiyar ya ce ya zuwa watan Nuwambar da ta gabata, an tabbatar da cewar kasashen duniya 44 sun yi nasarar kawar da cutar malariar baki daya daga cikin su, ya yin da wasu kuma ke ci gaba da daukar matakan cimma irin wannan nasarar.

Jami'in yace daga cikin kasashen duniya 83 da cutar tafi kamari a cikin su, 25 sun bayyana samun raguwar masu kamuwa da cutar, sabanin guda 4 kacal da aka gani a shekara ta 2000.

Ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kula da Afirka ya ce alkaluma sun nuna raguwar kashi 16 na yawan mutanen da cutar ke hallakawa tun daga shekarar 2015.

Hukumar lafiyar ta ce kasashe 11 da suka fi samun masu fama da cutar sun gudanar da taro a wannan shekarar inda suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar taka rawa wajen magance illar da cutar keyi, kuma sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da kuma Ghana.

Sauran sun hada da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Najeriya da Sudan da Tanzania da kuma Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)