Zauren taron Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yi zama ta musamman kan yaƙin Sudan

Zauren taron Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yi zama ta musamman kan yaƙin Sudan

Wannan yaki da ake fama da shi a Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, yayin da a hannu daya Majalisar ƊunniyaDD ke cewa shi ne rikici mafi muni wajen haifar da cikas ga  masu ayyukan jinkai a wannan zamani.

Duk da cewa yakin ya shafi mafi yawan jihohin kasar ta Sudan, amma fararen hula a El-fasher mai kunshe da mutane sama da milyan biyu a yankin Darfour, na daya daga cikin wadanda suka fuskantar kuncin rayuwa saboda yadda ‘yan tawaye suka yi masa kofar-rago.

Rikicin na Sudan dai na daga cikin batutuwan da za su fi daukar hankula a lokacin wannan taro na MDD, yayin da wasu ke ganin cewa lokaci ya yi domin sasanta shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar janar Abdel Fattah al-Burhan da abokin hamayyarsa Janar Mohamed Hamdan Daglo.

Babban magatakarda na MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa a game da halin da fararen hula suka tsinci kansu a Sudan, inda ya yi kira  ga bangarorin biyu da su tsagaita wuta tare da shiga tattauna domin sulhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)