A Landan Babban birnin kasar Ingila dubunnan mutane sun taru tare da gudanar da zanga-zangar la'antar kisan bakar fata George Floyd da 'yan sandan Amurka suka yi a garin Minnesotta bayan sun kama shi.
Masu zanga-zangar da suka taru a dandalin Trafalgar, sun dinga fadin "Idan ba adalci ba zaman lafiya", "Ku janye cinyoyinku daga wuyanmu", inda suka kuma dinga daga allunan adawa da gwamnatocin Amurka da Ingila.
Daga baya masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke unguwar Vauxhall.
Masu zanga-zangar da 'yan sandan Ingila da suka kewaye wajen, sun dinga musayar kalamai da ba hammata iska, inda aka kama mutane 11 a wajen.
Bayan janyewar 'yan sanda lamarin ya dan saukaka, amma masu zanga-zangar sun sake takawa zuwa Down Street, gaban ofishin Firaministan Ingila na "No 10" tare da yin wata zanga-zangar a nan ma.