Sojojin Labanan sun kaddamar da sintiri a cikin birnin Tarabulus, inda mutanen da ke zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma faduwar darajar kudin kasar suka toshe hanyoyi kuma suka bude wuta.
A cewar labaran kamfanin dillacin labarai na kasar na NNA, matasa dauke da makamai sun yi zanga-zanga a Tarabulus a arewacin kasar saboda faduwar darajar kudin Labanan a kan dala a kasuwar bayan fage da karuwar farashin kayayyakin masarufi da yawa da karin katsewar wutar lantarki.
Matasan wadanda suka toshe hanyoyi a sassa daban-daban na birnin don yin zirga-zirga sun nemi masu shaguna da su rufe shagunansu kuma suka bude wuta a sama na wani lokaci.
Bayan masu zanga-zangar sun bude wuta a sama, an ga sojoji suna sintiri a cikin garin da motoci masu sulke.