A Ireland rikici ya barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna adawa da sabbin matakan yaki da cutar corona (Covid-19).
'Yan sanda 3 sun ji raunuka kuma an tsare mutane 23 yayin afkuwar lamarin.
Masu zanga-zangar sun shirya gudanar da zanga-zangar a wani wurin shakatawa a tsakiyar babban birnin kasar, Dublin amma 'yan sanda ba su yarda ba.
Zanga-zangar ta rikide ta zama tashin hankali cikin kankanin lokaci; a rikicin da ya barke, ‘yan sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar da sanduna.
An tsare mutane 23, yayin da 'yan sanda 3 suka ji raunuka.
Firaministan Ireland, Micheal Martin ya bayyana zanga-zangar a matsayin rashin girmamawa ga wadanda suka sadaukar da kai sosai wajen yaki da cutar.