Zanga-zanga ta tsananta a Korea ta kudu duk da janye dokar Soji

Zanga-zanga ta tsananta a Korea ta kudu duk da janye dokar Soji

Karon farko kenan da shugaba Yoon ya yi yunƙuri amfani da dokar ta Soji tun bayan kawar da ita fiye da shekaru 40 da suka gabata, sai dai batun bai zo masa da daɗi ba ganin yadda ya ke ci gaba da ganin boren jama’ar ƙasar ba kaɗai daga masu ra’ayin kwamunisanci har da magoya bayan jam’iyyarsa mai ra’ayin ƴan mazan jiya.

Tsawon dare fusatattun al’ummar ta Korea ta kudu suka shafe kan tituna don nuna adawarsu da wannan doka, a wani yanayi manyan ƙawayen ƙasar ciki har da Amurka suka yi gum da bakinsu.

Dubban masu zanga-zangar sun yi ta kiraye-kirayen buƙatar murabus ɗin Yoon Suk Yeol, shugaba kuma tsohon lauyan da ya ɗare kujerar mulkin ƙasar a 2022.

A wani lamari mai kama da al’amara anga yadda rikici ya ɓarke a zauren majalisar har da shigowar Soji waɗanda suka yi taƙaddama da ɓangaren adawa da ke ƙalubalantar wannan doka ta shugaba Yoon.

Duk da cewa tuni Yoon ya sanar da janye wannan ƙudiri bayan faɗawar ƙasar wani yanayi da ba a taɓa gani ba, duk da haka ɓangaren adawa na neman lallai shugaban ya yi murabus, bisa kafa hujja da cewa bai cancanci ci gaba da shugabancin ƙasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)